'Yan Tawaye Sun Kama fadar Shugaba Gadhafi, amma

Hayaki ya cika sararin samaniyar birnin Tripoli, bayan fada da ya kaure a fadar shugaban kasa.

Mazauna birnin Tripoli, babban fadar kasar Libya, suna cike da murna da annashuwa da bukukuwa, duk da cewa ba a ga alamun shugaba Moammar Gadhafi ko iyalansa ba.

Mazauna birnin Tripoli, babban fadar kasar Libya, suna cike da murna da annashuwa da bukukuwa, duk da cewa ba a ga alamun shugaba Moammar Gadhafi ko iyalansa ba, bayan da ‘yan tawaye suka kama gidansa, suka gano makamai, akwatunan talabijin, da ma wasu kayan tsaraba.

Kai wa gidan shugaban kasar (Bab-al-Azaziya) farmaki da ya juma a matsayin cibiyar ikon mulki na Gadhafi, ya biyo bayan gwabza fada na kwanaki uku a birnin, wadda ta bakin shugaban majalisar gudanawar ta gwamnatin wucin gadi ta ‘yan tawayen kasar, ya halaka mutane fiyeda dari hudu, da jikkata wasu dubu biyu. Bai fayyace ko wan nan adadi na duka sassan biyun ne ko a’a.

Haka kuma Jalil, ya gayawa tashar talabijin ta France-24, cewa an kama sojoji magoya bayan Gadhafi, su dari shida, amma kamar yadda yace yakin bai kare ba, har sai bayan sun kama shugaban Libyan da kansa. Babban kwamandan ‘yan tawaye a Tripoli, Abdel-Hakim Belhaj, ya fada a yammacin jiya talata cewa, har yanzu akwai wani dan karamin sashe na makeken gidan Gadhafin dake hanun gwamnati.

Sa’o’I bayan barkewar fada, wata tashar talabijin kasar, ta ambaci Gadhafi yana cewa, kauracewa fadar shugaban kasa (Bab al-Aziziya) jada baya ga rago ne, sabo da farmaki da boma-bomai da NATO take kaiwa kan gidan ne. Tashar talabijin ta Al-Rai, ta bada labari laraban nan, cewa Gadhafi yayi jawabi ga al’umar kasar ta wata tashar rediyo, yana cewa yayi alwashin yin shahada, ko kuma samun galaba, kan abinda ya kira takalar NATO.

Anyi musayar harbe harben da bindigogi a fadar kasar ranar talata, har mayaka masu biyayya ga Gadhafi suka rufe manema labarai a O’tel da suke.

Ahalin yanzu kuma, mazauna birnin Zuara dake kusa da kan iyaka da Tunisia, sunce sojoji dake biyayya ga Gadhafi suna ci gaba da luguden wuta da bindigogin igwa da rokoki kan birnin.