‘Yan tawayen sun ce sojojin sun kuma kai hari shaguna da kuma kan wasu motoci a yankin na Kidal.
Washignton D.C. —
Wata gamayyar kungiyoyin ‘yan tawaye da ke yakar gwamnatin Mali a ranar Asabar ta zargi sojoji da dakarun tsaron Wagner na kasar Rasha da kashe fararen hula 11 a farkon makon da ya gabata.
Gwamnatin Mali ba ta ce uffan ba da kamfanin dillancin labarai na AFP ya nemi ya ji ta bakinta kan zargin kungiyoyin na ‘yan tawaye wanda suka fitar cikin wata sanarawa.
Kungiyoin sun zargi dakarun na Wagner da sojojin Mali da kai hari wani kauye da ke arewacin yankin Kidal.
A cewar ‘yan tawayen, fararen hula da aka kashe su 11, an tsinci gawarwakinsu a kone sannan wasu fararen hula biyu sun bata.
‘Yan tawayen sun ce sojojin sun kuma kai hari shaguna da kuma kan wasu motoci.