‘Yan Takarar Manyan Jam’iyyu A Najeriya Sun Jinkirta Fara Yakin Neman Zabe

Zaben Najeriya

Duk da bude damar fara yakin neman zabe da hukumar zaben Najeriya ta INEC ta yi, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da ke alwashin shiryawa tsaf don tinkarar zaben 2023 ba su kaddamar da kamfe ba.

ABUJA, NIGERIA - A zahiri dalilan jinkirin sun saba da na yadda a ka saba gani, inda wata jam’iyya ke jiran wata ta fara kamfe don samun damar gano logar abokiyar hamayyarta.

A zaben shekarar 2019, jam’iyyar APC ta caccaki dan takarar PDP Atiku da cewa ya na son sayar da Najeriya ga abokansa, bayan da ya ce in an zabe shi zai sayar da jarin kamfanin man NNPC.

A wannan karo APC ta bayyana cewa ta na son fadada sunayen jami’an yakin neman zabenta ne, ba tare da ambatar labarin fita ketare da dan takararta Bola Tinubu ya yi ba.

Yakin neman zaben APC, a ta bakin jigon tafiyar jam’iyyar Ibrahim Masari, na nuna cewa in APC ta zarce zata saka wa wadanda suka yi mata hidima, wanda hakan sauyi ne daga yadda gwamnatin Buhari ta ke tafiya a halin yanzu.

A bangaren Atiku Abubakar na PDP, wanda ke jihar Enugu ‘yan sana’o’i gabanin sanarwar dakatar da kaddamar da yakin neman zabe a Abuja, ya fi maida hankali ne wajen shawo kan yankin kudu maso gabashin kasar inda tsohon mataimakin takararsa Peter Obi ya fito, wanda a yanzu shi ke takara a jam’iyyar Labour. Bayan haka ya karfafa hulda da tsaohon shugaban jam’iyyar Uche Secondus daga jihar Rivers, saboda sa-in-sar da ake yi tsakaninsa da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, don rage kaifin illar da hakan zai jawo masa.

Shi kuma Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, yana ci gaba da gudanar da taruka da ‘yan jam’iyyarsa don kara karfafa tasirinta, inda har jigon jam’iyyar Buba Galadima ya ce in har Kwankwaso bai lashe zabe kai tsaye ba za a iya kai wa zagaye na biyu. Kwankwaso dai a kullum ya kan ce ya san kabli da ba’adin takarar siyasa.

Hukumar zaben INEC, a ta bakin jami’ar yada labaranta Zainab Aminu, ta ce yanzu yakin neman zaben gwamnoni da ‘yan majalisar jiha ne ke tafe a watan gobe.

Tun bayan zaben shekarar 2007, inda Olusegun Obasanjo ya sauka saboda karewar wa’adinsa bayan gaza tazarce karo na uku, sai a 2023 ne za a maimaita lokacin da za a yi zabe ba tare da shugaban da ke kan mulki a jerin ‘yan takara ba.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Takarar Manyan Jam’iyyu Sun Jinkirta Fara Yakin Neman Zabe