'Yan Takarar Da Za Su Fafata a Zaben Zagaye Na Biyu a Nijar

Bazoum Mohamed

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PNDS mai mulki Mohamed Bazoum zai kara da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane na jam’iyyar RDR a zaben zagaye na biyu da za a yi a watan Fabrairu.

‘Yan takarar biyu za su nemi kuri’ar jama’a bayan da suka gaza samun kashi 51 na kuri'un da aka kada a kokarin da suke yi na maye gurbin Shugaba Mahamadou Issoufou wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Bazoum ya samu kashi 39.33 yayin da Ousmane ya samu kashi 16.99.

Kashi 69 ne cikin mutum miliyan 7.4 da suka yi rijista, suka fita zabe a ranar 27 ga watan Disambar bara.

Bisa tanadin da doka ta yi, ‘yan takara biyu na farko da suka fi yawan kuri’a ne za su fafata a zagayen na biyu.

Hakan na nufin an zubar da mutum 28 kenan cikin ‘yan takara 30 da suka kara a zagaye na farko.

Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar

Da ma dai tarihi ya nuna cewa, zaben Nijar sai ya shiga zagaye na biyu kafin a samu wanda zai lashe shi.

A wannan gaba ne kuma ‘yan takarar biyu za su fara zawarcin jam’iyyun da za su yi hadaka da su domin lashe zaben a zagaye na biyu.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wata jam’iyyar da ta nuna aniyar kamawa kowane daga cikin ‘yan takarar biyu.

Sai dai tun gabanin zaben zagaye na farko, jam’iyyar PNDS na tunkahon tana da jam’iyyu sama da 50 da suke goyon bayanta yayin da gab da zaben, babbar jam’iyyar adawa ta Moden Lumana ta ce magoya bayanta su zabi Ousmane.