'Yan Ta'adda Sun Bad Da Kamanni Sun Kashe Sojojin Amurka

Gawar sojan Amurka

Gawar sojan Amurka

An kashe wasu sojojin Amurka biyu a bakin daga, a wani al'amarin da ake ganin irin harin nan ne na sojoji masu canza sheka.

Hadakar sojojin da NATO ke jagoranta, jiya Litini tace sojojin Amurka biyu ne kadai aka kashe, ba tare da ta yi cikakken bayani ba saboda ana so a sanar da iyalansu tukunna.

Daga bisani wani jami'in Amurka ya tabbatar da kisan mutanen a matsayin irin na sojojin nan masu canza sheka, inda wani sojan Afghanistan, ko kuma wani maharin da ya yi shigar burtu a kakin sojojin Afghanistan, ya bude wuta kan sojojin Amurka da na kawayenta.

Irin fahimtar da Amurka ta yi ma al'amarin da farko, ya biyo bayan irin ikirarin da mai magana da yawun Taliban Zabihullah, ya yi ta kafar twitter, inda yace Amurkawan sun mutu ne bayan da wani sojan Afghansitan da ya rikide ya bude masu wuta a wani sansanin sojan da ke kudancin lardin Kandahar.