SOKOTO, NIGERIA - A can baya mazauna yankunan karkara ne suka fi fuskantar hare haren ‘yan bindiga inda da yawansu ke hijira zuwa birane, amma yanzu biranen ma basu tsira ba daga hare haren ‘yan bindiga a wasu sassan Najeriya.
Jihar Sokoto da ke arewa maso gabashin kasar, na daya daga cikin jihohin da ke da yankuna masu fama da matsalar tsaro wadda sannu a hankali ke kara kusanto birnin jihar, musamman duba da sabon harin da aka kai a unguwar Gagi, bayan wasu hare hare da aka kai a wasu unguwanni da ke dab da mashigar birnin a kwanan nan.
Jagoran ‘yan banga na yankin Nura Bala, ya tabbatar da aukuwar harin na unguwar Gagi da ya ce sun fatattaki ‘yan bindigar bayan da suka yi musayar wuta da su.
Rundunar 'yan sandan jihar dai ba te ce uffan ba game da hare haren na baya baya, sai dai masana lamurran tsaro irinsu Dakta Yahuza Ahmad Getso na cewa irin wadannan hare haren a birane suna nuna matakan da mahukunta ke dauka don dakile ayyukan ta'addanci basa aiki.
Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da daidaita yankunan Najeriya duk da alkawarin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jima yana yi wa ‘yan kasa kan magance matsalolin kafin karewar wa'adin mulkinsa.
A saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5