Kungiyoyi da gwamnatocin Amurka da na Birtaniya duk sun yi tur da arangaman da ya auku tsakanin magoya bayan NDC jam'iyyar dake mulki da NPP jam'iyyar adawa wanda yayi sanadiyar kai hari gidan dan takarar adawan.
Rahotanni da suka fito daga Ghana sun nuna an yi amfani da kai harin kan gidan dan takarar da wasu muggan makamai.
Ofisoshin jakadancin Amurka da na Birtaniya sun kira a kai zuciya nesa a kuma yi kokarin samun zabe mai adalci cikin kwanciyar hankali. Suna kira a tabbatar da zaman lafiya.
Dangane da wannan arangamar Amurka ta bayyana bakin cikinta da abun da ya faru. Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka tace suna allawadai da duk wani tashin hankali da ya faru sanadiyar zaben dake zuwa. Tace yakamata 'yan kasar ta Ghana su kaucewa duk wani tashin hankali a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da zabe ranar bakwai ga watan gobe.
Amurka ta kira 'yan takaran da magoya bayansu da su gujewa duk abun da ka kawo tashin hankali lokacin zabe da kuma bayansa. Ta kirasu su warware duk wani rikici dake tsakaninsu ta hanyar shari'a.
To saidai jakadan zaman lafiya na zaben kasar Ribadu Ibrahim da aka tambayeshi akan lamarin sai yace ba'a tabbatar da gaskiyar maganar ba amma ya kara da cewa mutane su rungumi zaman lafiya su guji tashin hankali.
Ga rahoton Baba Makeri da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5