Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kasa Da Kasa Ta Yankewa Wani Mutum Hukunci Mai Tsanani


Ahmad al-Faqi al-Mahdi
Ahmad al-Faqi al-Mahdi

A wannan babban hukuncin da ba’a taba yanke irinsa ba, kotun kasa da kasa ta duniya a jiya Talata ta yankewa wani mutum mai tsaurin ra’ayin musulunci hukunci bayanda ta same shi da laifin nakkasa wasu kayan tarihi masu muhimmanci a kasar Mali.

Wannan ne karo na farko da kotun da mazauninta yake a Hague ta yanke irin wannan hukuncin laifin barna a matsayin laifin yaki kuma ta yankewa Ahmad al-Faqi al-Mahdi hukuncin daurin shekaru tara a gidan yari.

Laifin da Al-Mahdi ya aikata ya isa a yanke mishi hukuncin har shekaru 30, to amma kotun tayi la’akari da amsa laifinsa da kuma nuna nadamansa a kan abin da kuma gargadinsa ga sauran musulmi kada wani ya sake maimaita irin wannan danyen aikin.

An dora masa laifin jagorancin lalata tsofaffin masallai da aka gina tun daruruwar shekaru ta hanyar anfani da gatari da kuma injunan motocin bulldoza a birnin Timbuktu mai cike da a yayid da kungiyar tsagerun Islama suka kwace yankin arewacin Mali a shekarar 2012.

Mazauna birnin na Timbuktu da suka shedi rusa wannan wurin ibadar sun barke da Shewa lokacinda suka ji hukuncin da aka yanke mishi. Wani jagoran yan yawon bude ido ya shaidawa kampanin dillancin labaran Faransa cewa ko shakka anyi wa kakaninsu adalci da wannan hukuncin da aka yanke kan Mahdi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG