Tsohon ministan yayi wannan bayanin ne a wurin wani taron cin abincin da shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Bauchi ya saba shiryawa kowace shekara a jihar Kaduna.
Ya kuma jaddada cewa, kasancewar Allah ya kasa al'ummar Najeriya masu addinai daban-daban kuma karkashi kabilu mabanbanta alkahiri ne da ya kamata mu ribace shi ta hanyar hada kawunan mu.
Yayi bayani a game da babban zaben kasar da aka gudanar tsakanin watan biyu da watan jiya inda ya ce duk da cewa an kammala zabe, zaben ya bar baya da kura kuma kamata yayi mutane su kiyaye duk wani abinda zai raba kansu.
Shararren malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Bauchi a cikin jawabinsa a wurin taron, yace duk dan siyasar da zai hada kan al'umma ba tare da nuna banbanci ba, shi ya dace da shugabancin Najeriya, kana ya nuna cewar Allah ya hallice mu domin mu fahimci juna sannan mu taimakawa juna ba domin raba kawunan mu ba kuma ya ce duk wanda yake ji ba ayi mishi adalci ba a zaben da aka gudanar, kotu ce sahihin hanyar da doka ta tanadar domin neman hakkin mutum.
Pastor Yohana Buru wanda shi ma ya hallarci taron cin abincin da aka yi a gidan shahararren mallamin, ya ce kamata yayi mutane su yiwa Allah godiya da ya yadda Allah ya hallice mu kuma su fahimci masu neman janyo rarrabuwar kawuna a cikin al'umma.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5