‘Yan Shi’a, mabiya El-Zakzaky, sunyi zanga zangar neman a sako shugaban nasu da wa’adin sakinsa daga babbar kotun tarayya, ya cika bayan kwana arba’in da biyar.
Sakataren sashen dalibai na kungiyar, Abdullahi Musa, yayi jawabi a gaban hukumar kare hakkin Bil-Adam, ta Najeriya, a Abuja, inda ya bukaci jami’an tsaro su saki El-Zakzaky.
Yace matakin da kungiyar Shi’a, ta dauka mataki na lumana wanda tsarin mulkin kasa ya yadda dashi na zuwa kotu, kuma ta yanke hukunci cewa a sake shi cin kwana araba’in da biyar, da gina masa gida a inda yake so da bada diyyar Naira miliyan hamsin amma babu wani abu da Gwamnati tayi kawo yanzu.
Jami’an tsaro, basu takurawa masu zanga zangar ba har suka kammala korafen nasu.
Daraktan, kare hakkin Bil-Adam, na hukumar Nasiru Ladan, yace dama hukumar ta taba duba lamuran ‘yan Shi’an, har ta gayyaci shugaban Sojoji, haka wannan karon ma hukumar zata duba wannan lamari domin baiwa Gwamnatin Najeriya Shawarar abinda ya dace, daraktan yace idan Gwamnati bata yadda da hukuncin babbar kotun ba sai ta dauki mataki na gaba.
Your browser doesn’t support HTML5