'Yan Sandan New York Sun Daina Leken Asirin Musulmai

'Yan sandan birnin New York.

A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar New York ta fitar tace ta daina leken asirin al'umman Musulmai dake zaune a jihar.
Ma'aikatar 'yan sandan jahar New York ta fada a jiya Talata cewa ta rufe wani sashen ta na boye, na 'yan sandan ciki, masu aikin leken asirin Al'ummar Musulmin da ke zaune a jahar ta New York.

'Yan rajin kare hakkokin jama'ar jahar ta New York ne suka izawa shirin leken asirin wuta gami da zargin cewa ma'aikatar 'yan sandan ta tauye 'yancin walawa da sakewa.

Shirin ya dogara ne a kan 'yan sandan ciki, masu labewa a kantunan saida litattafai da wuraren cin abinci da kuma Masallatai su na satar jin maganganun da mutane ke yi.

Rundunar leken asirin da ake kira sashen kula da tattara bayanan jama'a da wasu jinsuna na musamman, ta na gudanar da ayyukan ta a unguwanni da dama a ciki da wajen birnin New york, ta kan yi nazari tare da lura da wuraren addini, da kungiyoyi, da wuraren shakatawa, da kuma duka al'amuran rayuwar jama'a ta yau da kullum.

Wasu rubuce-rubucen da kamfanin dillancin labaran Associated Press yayi ta yi a shekarar dubu biyu da goma sha daya bi da bi ne suka tona asirin shirin na 'yan sandan New york da aka kirkiro a wani kokarin saka idanu kan unguwannin da ka iya haifar da 'yan kananan kungiyoyin ta'addanci. An yi ta bibiyar daidaikun mutane da kungiyoyi ko da kuwa babu shaidar da ta nuna cewa su na da alaka da ta'addanci ko da aikata laifi.

Daga wannan lokaci ne Al'ummar Musulmi da kungiyoyi daban-daban na kare hakkokin jama'a suka tashi haikan suka bukaci da lallai sai a dakatar da shirin.