Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin da Ya Kashe Yahudawa Uku Ya Bayyana a Kotu


Hanyar shiga harabar yahudawa.
Hanyar shiga harabar yahudawa.

A karon farko mutumin da ya kashe wasu mutane uku a harabar yahudawa a jihar Kansas ta nan kasar Amurka ya bayyana a kotu

Mutumin da aka tuhuma da kaiwa Yahudawa mummunan harin da yayi kisa a jahar Kansas yayi bayyanar farko a kotu a jiya Talata.

An tuhumi Frasier Glenn Cross dan shekaru 73 da aikata kisan kai. Idan laifin ya tabbata, zai iya fuskantar hukuncin kisa.

Za a iya belin Cross da dola miliyan 10. Kuma an tsaida cewa zai sake bayyana a gaban kotu a ranar 24 ga watan nan na Afrilu.

Lauyoyin gwamnatin Amurka masu shigar da kara sun ce suna so syi amfani da dokar gwamnatin tarayya ta tuhuma da aikata laifi saboda tsanar wani jinsi, kuma suka ce nan kusa za su gabatar da shaida a gaban ayarin masu taya alkali yanke hukunci. Wannan ma na iya zama wata shari'ar da za a yankewa hukuncin kisa.

Frazier Glenn Cross tsohon soja ne da yayi yakin Vietnam kuma dadadden mai akidar fifita jinsin farar fata akan kowane jinsi, har wa yau kuma dan kungiyar Ku Klux Klan ne mai akidar dankwafe bakaken fata ta hana su farcen susa a kasar Amurka. Da aka kama shi a ranar lahadi bayan kashe-kashen, ya furta wasu kalaman taken 'yan Nazi da kuwa, a gaban kemarorin talbijin.

Sakataren shari'ar Amurka Eric Holder ya bukaci majalisar dokoki ta amince da wasu kudade dola miliyan 15 da za a yi amfani da su wajen horas da 'yan sanda a koya mu su dabarun yin maganin masu harbin mutane.

Ma'aikatar shari'a ta ce Holder ya gabatar da bukatar ce bayan abun da ya faru a Kansas da kuma harbin da aka yi ranar 2 ga watan Afrilu a sansanin sojojin Fort Hood na jahar Texas, wanda ya halaka mutun hudu.
XS
SM
MD
LG