Wasu jami’an ‘yan Sanda dari bakwai da sittin da bakwai sun samun horo na masamman a cibiyar horar da dabarun shugabanci da zama dan kasa na gari a Shere Hill, dake birnin Jos.
Jami’an ‘yan Sandan masu matsakaicin mukamai daga kwalejin horar da ‘yan Sanda dake Jos, sun yi mako uku a cibiyar horar da dabarun shugabanci da zama dan kasa na gari inda suka samu horo akan matakai daban daban na kwarewa a aikin su da inganta dangantakarsu da al’uma.
Darakta a kwalejin horar da jami’an ‘yan Sanda dake Jos, D C Aminu Alhassan, yace horon da aka baiwa jami;an na ‘yan Sanda yana da mahimmanci kwarai, yana mai cewa dan Sanda yana cikin mutanen da ya kamata irin wannan horon saboda abune wanda zai sa mutun ya jurewa wahala da sai ya cimma abinda yake nema, saboda haka idan basu yi wannan ba yaya zasu sa wasu suyi ko kuma su jagorance su, ba za a samu nasara ba.
Shugaban cibiyar horar da dabarun shugabanci sa zama dan kasa na gari Abdulmumini Mamako, yace suna bada horo ne ta yarda al’uma zasu zama ‘yan kasa na gari, da kara inganta dangantakarsu da jama’a.
Your browser doesn’t support HTML5