Yan Sandan Najeriya Sun Afkawa Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Jahar Bayelsa

Dan Sandan Najeriya

Hedikwatar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce rundunar kai daukin gaggawa dake karkashin ofishin Sifeto Janal na ‘yan sandan kasar ta afkawa gungun wasu masu sace mutane da suka dade suna addabar al’ummar yankin Niger Delta.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa matsalace da ta dade tana addabar al’ummar jahohin Rivers da Bayelsa da kuma yankin Niger Delta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya kuma mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jahar Bayelsa, Don N. Awunah, yace jami’ansu da suka fito sintiri sunyi hadu da gugun masu garkuwa da mutane bayan da rahotannin sirri suka nuna cewa son sace wasu manyan mutane.

A dai dai lokacin da masu garkuwa da mutanen ke kokarin yiwa jami’an tsaron kwantan bauna ne ‘yan sanda suke bude musu wuta, inda suka jikkata uku daga cikinsu suka kuma kame wani matashi mai shekaru 30 mai suna James Peter, dan asalin jahar Bayelsa wanda ke taimakawa da jami’an da muhimman bayanai.

An dai sami wasu miyagun makamai tare da su wanda suka hada da miyagun makamai masu aman harsashe da bindiga kirar AK 47 guda 4 da kuma sauran wasu makamai.

Najeriya tana daga cikin manyan kasashe uku a duniya wajen garkuwa da mutane a cewar masanin tsaro Aliko El-Rashid Harun, biyo bayan kasar Mexico da India. Haka kuma yace ta kasance kasa ta daya a nahiyar Afirka.

Masana na danganta tafka miyagun laifuka kamar fashi da makami da kuma garkuwa da mutane ga matasa sakamakon shan miyagun kwayoyi. Shugaban hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriya, Dakta Garba Abari, yace yawacinsu matasa ne cikin halin maye ke aikata irin wannan laifi.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Yan Sandan Najeriya Sun Afkawa Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Jahar Bayelsa - 2'25"