Da yake gabatar da wadanda aka kaman ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Filato, Mathias Tyopev, ya ce 13 daga cikinsu ana zarginsu ne da hannu dumu-dumu kan kisan janar din, yayin da wassunsu sun gani ko sun ji abin da ya faru amma suka ki kai rahoto wa jami’an tsaro.
Jami’in ‘yan sandan ya ce shida daga cikinsu wadanda suka hada da sarakunan gargajiyan yankin guda biyu, sun kawo kansu ne wa ‘yan sanda bayan an bayyanasu a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo, yayin da ya ce suna kan neman mutane biyu da suma ke da hannu kan kisan janar Alkali.
Lauya dake Magana da yawun al’ummar yankin da aka ce an sami gawar janar din, Barista Godfree Mathew, ya ce sun gamsu da matakin da hukumar ‘yan sandan ta dauka na gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya.
A ranar asabar da ta gabata ne aka binne gawar janar Idris Alkali mai ritaya a Abuja.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5