Bisa ga sanarwar da aka ce sun fitar bayan sun tsige shugabanninsu, wai a zamansu na jiya zasu rubutawa gwamnan wasikar anniyar tsigeshi.
To saidai zaman nasu na jiya bai yiwu ba domin sun kasa gudanar da zamansu saboda yadda jami'an tsaro suka kulle kofar shiga majalisar tare da fatattakarsu da barkonon tsohuwa. Cikin 'yan majalisar da suka kasa shiga zauren taron har da sabon kakakin Onarebul Isa Kawu.
Abun da ya faru ya haifar da rudani matuka cikin jama'ar jihar tare da jefa ayar tambaya. Jama'a na mamakin yadda za'a hana 'yan majalisa 20 cikin 25 shiga zauren taron majalisar domin gudanar da aikinsu.
Sabon kakakin majalisar Onarebul Isa Kawu yace babu wanda yake da ikon hanasu shiga majalisar domin gudanar da aikinsu. Yace babu wanda yake da wannan damar. Da aka gayawa sabon kakakin cewa watakila 'yansanda sun yi hakan ne domin wai zasu rubutawa gwamna takardar gargadin tsigeshi sai yace menene hujjar. Yace shi bai ga wata takardar tsige gwamna ba.
Anfani da barkonon tsohuwa ya tayarwa 'yan majalisar hankali. Onarebul Bello Agwara sabon mataimakin kakakin majalisar yace dukansu barkonon tsuhuwar ya shafa.
Amma rundunar 'yansandan jihar tace ta tura jami'anta harabar majalisar ne domin tabbatar da tsaro kamar yadda kakakin rundunar Ibrahim Gambari ya bayyana. Yace akwai rahotanni da suka samu dake cewa akwai wasu mutane dake yiwa majalisar barazana saboda haka wai sun je majalisar ne domin kare rayuka da dukiya.
Ita ma gwamnatin jihar ta nisanta kanta daga rikicin majalisar. Kwamishanan labarai Danladi Ndayabo ya shaidawa Muryar Amurka cewa gwamnatin jihar bata da hannu a rikicin.
A wata sabuwa kuma wata kotun jihar ta hana 'yan majalisar daukan duk wani matakin tsige gwamna Mua'zu Babangida Aliyu. Alkalin kotun mai shari'a Idris Ebuti ya tsayar da ranar 27 ga wannan watan a ranar sauraren karar da gwamnan ya shigar kotun domin neman a hana 'yan majalisun daukan matakin tsigeshi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5