An kammala taron kwanaki bakwai da aka gudanar domin duba hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi yankin masarautar Kontagora dake jihar Neja.
Attajirai da 'yan bokon masarautar da yawansu ya kai dubu da ashirin da takwas suka halarci taron.
Manyan matsalolin da suka addabi masarautar sun hada tabarbarewar ilimi, karancin kayan more rayuwa, da kuma rashin tsaro da ya kaiga sace jama'a. Ko a ranar Juma'a da ta gabata wasu 'yan bindiga sun yi awangaba da kanin mataimakin gwamnan jihar mai suna Alhaji Ayuba Ibeto.
Saidu Ibrahim daya cikin wadanda suka shirya taron ya yi karin haske. Yace akwai matsalar sace-sace. Akwai kuma sabuwar matsala da ta kunno kai ita ce ta sace mutane. Yace a kasar Mariga akwai matsalar satar shanu da sauran wasu abubuwa.
Mahalarta taron sun ce ba siyasa suke yi ba. Yace sun tsara taron ne tun da dadewa amma sai gashi ya fara gaf da ake shirin canjin gwamnati. Sun dade suna kuka amma kukan nasu bai kai ba. Amma yanzu danuwan kukan nasu ragamar mulki zata shiga hannunsa. Yace suna gani lokaci yayi da Allah cikin ikonsa zai share masu hawaye.
Mahalartan taron sun shaida cewa ba'a taba zama an yi nazari akan matsalolin da masarautar Kontagora ke fuskanta ba a fannonin rayuwar dan Adam. To amma yanzu ga mulki zai shigo hannunsu saboda haka ba zasu zauna kara zube ba basu kawo abubuwan da zasu taimaki gwamnatin da zata shigo ba.
Masarautar garin Kontagora ta yaba da masu shirya taron tare da fatan an samu biyan bukata. Wakilin Sarkin Kontagoran yace abubuwan da aka tattauna akansu abubuwa ne da zasu sa kasar ta cigaba.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.