Wani ibtila'i ya afku a karamar hukumar Biase ta jihar Cross Rivers yayin da aka kashe wani Bishop da wani masanin tarihi a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a yankin.
Baise karamar hukumar ce ta asali ga mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Ivana Esu.
Kisan yana cikin zazzafar rikicin kabilanci tsakanin kabilun Abanwan da Urugbam a cikin kabilar Erei.
An kona Bishop din da ransa kuma aka fille kan dansa a wani sabon yakin kabilanci da ya shafi al'ummomin biyu.
Wasu majiyoyi daga al’ummar da suka yi magana kan tsauraran sharudda na sakaya sunansu sun bayyana cewa an yi wa Bishop din kwanton bauna ne tare da dansa a kan babur a kan hanyar su daga unguwar Abanwan zuwa Afikpo da ke kusa da jihar Ebonyi.
Al’ummar Erei dai sun shafe shekaru suna takun saka a kan wani fili da rusassun yankin Gabashin kasar ya kafa kafin yakin basasar Najeriya a matsayin matsugunin na gonar ‘ya’yan manja.
An mika matsugunin ga gwamnatin jihar Cross River jim kadan bayan yakin basasar Najeriya na 1967 zuwa 1970, ganin cewa wurin yana cikin jihar.
Sai dai al’ummar Erei, inda ake noman ‘ya’yan manja, na da kauyuka 10, wadanda a yanzu haka suke neman mallakarsu.
A halin da ake ciki yanzu, hukumomin tsaro daga hedikwatar rundunar soji ta 13 ta Calabar, ta tabbatar da tura sojoji a yankin Abanwan da Urugbam, domin kwantar da tarzomar