Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya barke akan gonaki tsakanin wasu al’ummomin garin Ukele cikin jihar Rivers da makwaftansu na kauyen Eze a jihar Ebonyi.
Tun a makon jiya ne suka soma rikicin da ya haddasa kashe kashe da kone kone a sassa daban daban na kauyukan.
Wani manomi mai suna Obong Bassey dake garin Ukele da lamarin ya shafa ya ce mazauna kauyukan manoman doya da shinkafa ne kuma rikicin ya faru ne akan mallakar filin gona da ya kai ga harbe wata mace a kafa. Daga nan suka soma kashe juna. Yace an tattaunawa a kauyen Ibole domin a samu zaman lafiya. Jami’an tsaro ma sun shiga tsakani.
Obong Bassey yace wadanda suka yi harbi basu halarci taron zaman lafiyan ba saboda haka babu wata yarjejeniya da aka kula. Rashin sanin tabbas ya sa suna zaman dar dar domin gudun abun da ka biyo baya.
Rikicin bashi ne na farko ba amma a wannan karon jami’an tsaro sun sha alwashin kawar da duk wata matsala.
Hafis Muhammad Inuwa kwamishanan ‘yan sandan jihar Cross Rivers ya ce akwai mace a cikin jihar Cross Rivers da ta je gona sai mutanen dake bangaren jihar Eboyin suka harbe ta a kafa. Wannan harbin shi ya tunzura mutanen Cross Rivers su ma suka fara harbe harbe. Ya ce ya yanzu gawa daya suka gani amma an kone gidaje da dama.
A saurari rahoton Lamido Abubakar Sokoto domin jin karin bayani
Facebook Forum