Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama tare da rubuta laifukkan fyde da ma wasu laifukkan da suka shafi fyde tun daga watan junairun shekarar 2017 zuwa yanzu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Magaji Majiya, ya bayyana wa manema labarai hakanne a lokacin da ake shagulgulan shigowar sabuwar shekara a jihar kano.
A shekarar 2016 an yi lissafin laiffukan fyde dari biyar da arbain da bakawai yayinda aka yi lissafin dari uku da talatin da hudu a shekarar 2017, inda ya ce an samu raguwar laiffukan fyde a shekarar 2017.
Mujallar Daily Post, ta wallafa cewa kakakin rundunar ya bada bayanin cewar rundunar ta rubuta manyan laiffuka dari shida da daya, kuma ta dawo da motoci talatin da biyar da aka sace tare da rubuta dukiya da ta kai har ta Naira, milliyan dari bakwai da arbain da hudu wadda ake ta bincike a kai.
Majiya ta jaddada cewa aukuwar laiffufuka ya ragu sosai duba da yadda aka yi shirin baza ‘yan sanda a jihar wanda ya taimaka wajen kama masu aikata laifuka da waddanda suke da hannu cikin aikata laifukan.