Rundunar 'yan sandan Najeriya ta shiga farautar dakataccen kwamishinan zaben tun bayan da hukumar zabe ta kasar wato INEC, ta yi watsi da sakamakon da ya bayyana na gwamnan jihar Adamawa, inda ya ce 'yar takarar gwamna ta jam'iyyar APC, Aisha Benani ce ta lashe zaben, gabanin a kammala tattarawa da kidaya kuri'un da aka jefa gaba daya.
Hukumar ta INEC ta matakin da Hudun ya dauka a matsayin wanda ya saba doka da ka'idar aiki, kuma wani abu da bai kamata ba.
Akan haka ne hukumar ta nemi babban sufeto-janar na 'yan sanda da ya kama Hudu Ari, tare da gudanar da bincike da kuma daukar matakin doka da ya dace da abin da ya aikata.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ta Najeriya CSP Olamuyiwa Adejobi ya ce wasu zaratan 'yan sanda na musamman dake sa ido da bin diddigi ne suka cafke dakataccen kwamishinan zaben a ranar Talata.
Ya kara da cewa a halin yanzu ana tsare dashi kuma ana yi masa tambayoyi
kan dalilin da ya sa ya yi abin da yayi a Adamawan.
Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya dai ya kara nanata cewa za'a ci
gaba da bibiyar wannan magana kuma duk wanda aka samu da hanu wajen
aikata ba daidai ba ko wanene kuma ko me girmansa za'a kamashi sannan a
gurfanar da shi gaban shari'a
Duk kokarin da wakilinmu a Abuja yayi don neman jin karin bayani kan lamarin daga rundunar 'yan sandan yaci tura, domin jami'an sun ce a halin yanzu bincike kawai aka fara don haka ba zasu yi riga mallam masallaci ba.