‘Yan Sanda Sun Datse Hanyar Isa Fadar Sarki Sanusi II Tare Da Takaita Zirga-Zirga

Fadar Masauratar Kano

A cewar wata majiya a masarautar ta Kano, jami’an tsaro dauke da manyan makamai, ciki har da motocin sulke, sun yiwa kofar shiga fadar kawanya, tare da takaita zirga-zirga.

Ana zaman dar-dar a Kano sakamakon zargin da ake yi na cewa ‘yan sanda sun datse hanyar isa Fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, inda suka hana shi halartar wani bikin sarauta a karamar hukumar Bichi.

Yayin bikin sarkin zai mika sandan girma ga sabon Hakimin Bichi.

A cewar wata majiya a masarautar ta Kano, jami’an tsaro dauke da manyan makamai, ciki har da motocin sulke, sun yiwa kofar shiga fadar kawanya, tare da takaita zirga-zirga.

Haka kuma, kokarin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shiga tsakani ya gamu da cikas, inda aka bada rahoton cewa an hana tawagar da ya tura shiga fadar.

A wani labarin mai nasaba da wannan kuma, jami’an tsaro sun killace wurin da za’a yi bikin sarautar na Bichi, abin da ya jefa baki da masu shirya taron cikin rudani.

Ko da aka nemi jin ta bakinsa, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa yaki cewa uffan, illa cewa “ba zan iya yin sharhi a kan batun ba a halin yanzu.”

Har ila yau, babu ko guda daga cikin gwamnatin Kano ko masarautar da ya fitar da sanarwa kan batun a hukumance.