Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Obianuju Odah, ta karyata adadin gidajen da aka kona, da cewa gidaje shida ne aka kona, ba gidaje 30 ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito.
Ta ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Awosola Awotunde da kansa ya ziyarci garin, don gane ma idanunsa gaskiyar lamarin, inda ya gana da masu ruwa da tsaki na garin da kuma wadanda al'amarin ya shafa. Ya kuma tabbatar musu cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen tabbatar da adalci da kuma cafke duk wadanda ke da hannun a rura wutar rikicin.
Ta dai kara da kira ga al'ummar garin da su taimaka gwargwadon hali, wajen kama wadanda suka haddasa rikicin, yayin da ta bada tabbacin cewa yanzu an samu kwanciyar hankali da lumana a garin.
Yanzu gwamnatin jihar ta ce tana kan daukar kwararan matakai, don magance irin wadannan tashin-tashina, kamar yadda Mista Emmanuel Uzor, mai magana da yawun gwamna Dave Umahi na jihar, ya shaida wa Muryar Amurka:
Ya ce, "Yanzu muna kan maganar ne. Gwanan jihar ya kafa kwamitin da zai binciki lamarin. Yau zai ziyarci garin da kansa don warware bakin zaren lamarin. Ya kuma bukaci ma'aikatun tsaro a jihar su zage dantse don magance matsalolin tsaro da kan barke tsakanin magoya bayan 'yan siyasa da kuma jam'iyyun nasu, musamman dai a wannan lokacin zabe.
Ga cikakken rahoton wakilin mu Alphonsus Okoroigwe a kan wannan batu:
Your browser doesn’t support HTML5