Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ba da umurni a ci gaba da yakin neman zabe har zuwa daren ranar Alhamis.
INEC ta dauki wannan matsayar ce, bayan da ta kammala wani taronta da ta yi a Abuja a jiya Litinin.
An shiga yanayi na kokwanto kan makomar yakin neman zabe, bayan da hukuamr ta INEC ta dage babban zaben kasar zuwa Asabar da ke tafe saboda wasu matsaloli da ta fuskanta.
Da farko wasu rahotanni sun yi nuni da cewa hukumar zaben ta ce ba za a ci gaba da kamfe ba.
Amma hukumar ta fayyace wannan lamari bayan taron da ta yi.
Tuni dai jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce za ta ci gaba da kamfen biyo bayan dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya zuwa ranar asabar 23 ga watan nan.
Shugaban APC Adams Oshomohle ne ya karanta wannan matsaya a jawabin bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ya samu halartar shugaba Buhari da uban jam’iyyar Ahmed Bola Tinibu.
Oshiomohle ya ce jam’iyyar ta bukaci gwamnati ta kafa kwamitin bincike don gano dalilan da su ka sa a ka dage zabe don gano ko akwai wanda ya yi zarmiya.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin jin karin bayani: