Mutane 3 sun mutu a musayar wuta yayin da hadin gwiwar sojoji da 'yan sanda suka dakile harin da wani gungun 'yan fashin banki mai mambobi 15 ya kaiwa reshen "First Bank" dake Abaji, a Abuja a jiya alhamis.
Sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yau Juma'a, tace samamen hadin gwiwar da dakarun soja dana 'yan sanda suka kai wurin da al'amarin ya faru ya dakile tagwayen hare-haren da 'yan fashin suka kaiwa cajin ofis din 'yan sanda da reshen First Bank dake Abaji a lokaci guda, inda suka yi amfani da gurneti a yunkurin yin fashi a bankin.
Sanarwar ta kara da cewar, jami'an tsaron sun yi zazzafar musayar wuta tsakaninsu da 'yan fashin, abinda ya tilasta musu arcewa da raunukan harsashi domin neman tsira.
Musayar wutar tayi sanadiyar kama 3 daga cikin 'yan fashin, da suka hada da, Usman ( wanda ba'a tantance sunan mahaifinsa ba), wanda rahotanni suka ce shine shugaban gungun 'yan fashin, da Nuhu Musa mai shekaru 41, da kuma Muhammad Aminu dan shekara 25, da raunukan harsashi daban-daban.
Fusatattun al'ummar gari sun cinnawa gawar daya daga cikin 'yan fashin wuta a wurin, bayan da jami'an tsaro suka hallaka shi.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5