'Yan Republican dake Neman Shugabancin Amurka Sun Yi Muhawara ta Uku

'Yan Republican da suka yi muhawara ta uku

Mutane 10 da suke neman jam'iyyar Republican tana nan Amurka ta tsaida takarar shugabancin Amurka sun kara kan manufofinsu kan tattalin arziki da kuma sukar junansu a muhawara ta uku da suka gudanar a daren jiya Laraba.

Muhawarar da tashar talabijin ta CNBC ta nuna kai tsaye, tazo ne yayinda aka fara ganin alamun koma baya ga mutuminda ya juma a zama na daya tsakanin 'yan takarar watau Donald Trump.

Yanzu dan kasuwan, yana baya ga tsohon likitan nan Ben Carson, wanda kuri'un neman jin ra'ayin jama'a a fadin Amurka suka nuna yana kan gaba, watakil haka ta sa Trump ya sassauta lafazinsa idan aka kwatanta da muhawarori da aka yi a baya.

Dr. Carson wanda yake da sassanyar muriya, wand a ba dan siyasa bane, ya sha suka daga abokanan takararsa,musamman kan shirin haraji daya gabatar, wanda yace ya samo asali ne da zakka,kamar yadda yake cikin Injila.

Gwamnan jahar Ohio John kasich ya caccaki manyan 'yan takarar biyu da suke kan gaba, ya kira shirin haraji da suka gabatar a "zaman wasan yara," ya kara da cewa bai dace ba "Amurka ba zata zabi mutane da basu da kwarewa a harkokin shugabanci ba".

Wata karawa da aka yi a farko farkon shine lokcinda tsohon Gwaman jahar Florida Jeb Bush ya soki lamirin dadadden abokinsa shima daga jahar Florida, Marco Rubio, saboda baya halartar zaman majalisar dattijai.

Ba tareda wani bata lokaci ba, Sanata Rubio ya maida martani, yace "wani ne ya shawarwaci Bush cewa sukar Rubio zata taimaka masa a siyasance".