A jamhuriyar Nijer wasu ‘yan kasar sun bayyana rashin jin dadi a game da cece kucen da ya biyo bayan gudunmowar motocin da Najeriya ta bai wa Nijer domin amfanin jami’an tsaron da ke ayyukan tabbatar da tsaro akan iyakokin kasashen 2, suna masu tunatarwa a game da girmar dadaddiyar dangantakar al’umomin kasashen biyu da kuma yadda gwamnatocin su ke taimaka wa juna idan bukata ta taso.
Rahotanni sun yi uni da cewa tun a watan Fabrairun da ya gabata ne mahukuntan Najeriya suka fitar da Naira biliyan don sayen motoci kimanin 10 da aka bai wa jamhuriyar Nijer a matsayin wata gudunmowar da za ta bada damar karfafa matakan tsaro akan iyakokin kasashen biyu.
To amma wannan hobbasar ta gwamnatin Muhammadu Buhari ta harzuka wasu ‘yan Najeriya dake ganin an yi abin a wani lokacin da askarawan kasar ke cikin babbar bukatar kayan aiki don tunkarar matsalar tsaron da ke kara yaduwa. To amma wani dan Nijar, Abba Dan Illela, ya ce a duk lokacin da daya daga cikin kasashen nan ta taimaka wa ‘yar uwarta tamkar yi wa kai ne.
Har ila yau masu korafi akan wannan al’amari sun bayyana damuwa a game da yadda aka yi komai cikin duhu saboda haka suke ganin alamar rashin gaskiya a tattare da hakan, abin da shugaban kungiyar Voix des sans Voix ke ganinsa a matsayin alamar yadda wasu suka jahilici mu’amula ta tsakanin Najeriya da Nijar.
Duk da cewa mahukuntan Najeriya sun yi bayani a wannan mako game da wannan tallafi, har ma da yadda aka bayar da odar wadanan motocin, batun na ci gaba da haddasa mahawwara a kafafen sada zumunta a tsakanin ‘yan Nijar da ‘yan Najeriya, abinda ya sa mai sharhi akan sha’anin tsaro, Abdourahamane Alkassoum, ke jan hankulan al’umonin wadanan kasashe su guji furta kalaman da ka iya mayar da hannun agogo baya a yakin da ake gwabzawa da ‘yan takife.
Najeriya da Nijar da ke da iyaka da tsawonta ya haura km sama da 1500 na matsayin ja gaba a rundunar hadin gwiwar da ke yaki da Boko Haram a yankin tafkin Chadi. Haka kuma kasashen 2 sun kafa wata hukumar hadin gwiwa ta Joint Commission a farkon shekarun 1970 dake da alhakin inganta hulda a fannoni da dama.
Saurari rahoton Souleyman Barma:
Your browser doesn’t support HTML5