Shugaban Nijar din kwana kwanan nan ya ziyarci kasashen Morocco da Equitorial Guineaa da Madagascar domin halartar taron shugabannin kasashe.
Malam Ibrahim Kantama wani dan Nijar mai kishin kasa yana jin ciwon al'amarin. Yace akalla a cikin wata shugaban kasar zai yi bulaguro sau goma. A tattara kudaden bulaguro goma cikin wata daya ai an banatar da ludin kasa, inji Ibrahim. Tafiye-tafiyen basu da anfani koda ma kudi yake samowa balantana ma ba haka ba ne. Baya samo komi.
Alhaji Ibrahim Yakuba ministan harkokin wajen kasar Nijar yace duk tafiyar shugaban ta yin taro ne kuma duka tarukan suna da mahimmanci. Yace wajibi ne a ce shugaban kasa ya je kuma yayi magana a gaban duniya. Taron baya bayan nan kasashe tamanin da wasu 'yan kai suka halarci taron. Cikinsu shugabani goma aka bari suka yi jawabi da suka hada da shugaban Nijar.
To saidai malama Ramatu wata dalibar jami'a na cewa su na kasashen waje sai sun tsaya sun yi aiki suke samun kudi ke nan ya kamata su ma su tsaya su yiwa kasarsu aiki maimakon yawo da kokon bara a hannu.
Wani abun da mazauna birnin Yamai ke korafi a kai shi ne yawan rufe hanyoyi na tsawon lokaci duk yayinda shugaban kasa zai yi tafiya. Wani yace watarana da shugaban zai yi tafiya cikin gidan gawa aka turasu sai da shugaban ya wuce aka sakesu. Sai a kawo jami'an tsaro a jibgesu tamkar ana yaki ne alhali kuwa tafiya ce shugaban kasa zai yi.
Ministan tsaron kasar yace saidai su nemi gafara daga jama'a tare da cewa su kara hakuri saboda tabarbarewar harkokin tsaro ya sa jami'an tsaro ke daukan tsuraran matakai da zara shugaban kasa zai yi tafiya.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5