'Yan Nijar mazauna arewa maso gabashin Najeriya sun tafi kasarsu yin zabe

Hoton kasar Nijar

'Yan asalin kasar Nijar mazauna arewa maso gabashin Najeriya da basu samu damar cika ka'idar kada kuri'unsu a Najeriya ba sun tashi zuwa kasarsu domin su yi zabe.

Wani dan Nijar Malam Ladan Mai Tukunyar Kaji jagoran tafiyar yace zasu tafi Nijar ne su kada kuri'unsu domin basu samu yin rajista a yankinsu na Najeriya ba. Duk wadanda suka shiga yin balaguron suna da rajista a jihohinsu can Nijar.

Wadanda suka bar shiyar arewa maso gabas a karkashin jagorancin Mai Tukunyar Kaji su 1172 ne.

Huseini Isa sakataren 'yan Nijar din na shiyar arewa maso gabas yace dukansu an dauka masu ababen hawan zuwa da dawowa.

Basu samu yin rajista ba saboda basu tafi Kano ba inda aka shirya yin rajistan.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Nijar mazauna arewa maso gabashin Najeriya sun tafi kasarsu yin zabe - 3' 36"