'Yan Najeriya Sun Ci Gaba Da Nuna Fusatarsu A Yau Talata

Matasa a fusace su na kona tayoyi da tarkace domin su nuna rashin yardarsu da janye tallafin farashin mai da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta yi, Lagos Talata, 10 Janairu 2012.

Dubbai sun yi gangami a fadin kasar domin nuna fusatarsu da janye tallafin farashin mai da kuma wawure dukiyar gwamnati da jami'an gwamnati ke yi.

'Yan Najeriya sun ci gaba da bayyana fushinsu a yau talata, a yayin da dubbai suka yi cincirindo a fadin kasar domin su nuna rashin yardarsu da tashin gwauron zabin farashin mai a kasar, da kuma zarmiya da cin hanci na jami'an gwamnati.

A wannan rana ta biyu ta yajin aiki a fadin kasar, 'yan sanda a Lagos, cibiyar harkokin kasuwancin kasar, sun tsaya suka zuba ido a yayin da dubban mutane suka yi gangami su na sukar lamirin gwamnati, yayin da hayaki ke tashi sama daga tayoyin da suka kona a kan hanyoyi. matasa dake fusace sun tayar da wuta a kan hanyoyin domin hana shiga cikin wata unguwa ta masu hannu da shuni.

Wasu dubban kuma sun yi gangami a Abuja, babban birnin kasar. Masu zanga-zanga a Abuja sun yi yawan da sai da aka tura karin 'yan sanda zuwa wurin gangamin domin tabbatar da tsaro.

A birnin Benin dake kudancin kasar, wasu mutane dake fusace sun kai farmaki a kan wani Masallaci da wata makaranta. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe mutane biyar. Wani jami'in kungiyar yace watakila wadannan hare-hare na Benin su na da alaka da rashin jituwar da ake fama da ita a tsakanin Musulmi da Kirista a kasar.

An bayar da rahoton mutuwar mutane uku a ranar farko ta gangamin yaki da janye tallafin farashin man fetur a jiya litinin.

Manyan kungiyoyin kwadago na Najeriya sun lashi takobin yin yajin aiki har sai gwamnati ta maido da talafin farashin man fetur da ta janye a ranar 1 ga watan Janairu. Janye tallafin farashin ya sa kudin man fetur a kasar ya ninku cikin kwana guda.

haka kuma, farashin abinci da na sufuri yayi tashin gwauron zabi tun daga lokacin da aka janye tallafin farashin man.

Aika Sharhinka