'Yan Najeriya Sun Bayyana Ra'ayoyi Mabanbanta Kan Shirin Farfado Da Tattalin Arziki

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari yayinda yake kaddamar da sabon shirin

Bayan da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kaddamar da wani sabon shirin farfado da tattalin arzikin kasar da zai fara aiki daga wannan shekarar zuwa shekarar 2020, 'yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta.

'Yan Najeriyar sun bayyana ra'ayoyin nasu ne yayin wani rangadi da Muryar Amurka ta yi a wasu sassan jihar Oyo dake kudu maso yammacin Najeriya.

Wani mazaunin jihar ta Oyo wanda ya bayyana sunansa a matsayin Abule ya ce sabon tsarin na da kyau amma akwai bukatar shugaban ya kara mayar da hankali kan hauhawan farashin kayayyaki.

Baya ga hauhawan farashin kaya, Abule ya yi zargin cewa akwai 'yan majalisu dake yi ma shugaba Buhari zagon kasa, lamarin da ya ce ya na dagula lissafi.

Shi kuwa Manuga wanda dan jam'iyyar PDP ne ya ce sun ji dadi domin akwai wasu tsare-tsare masu yawa da ya yi kamar cewa za'a gyara hanyoyi domin a samu wadatar arziki da gyara wutar lantarki domin a samu aikin yi.

Sai dai ya ce a mafi yawan lokuta ire-ire wadannan alkawura ba a samun cika wa.

Abubakar Muhammad mataimakin sakataren kungiyar manoma ya ce shugaba Buhari ya na kokarin inganta tattalin arzikin Najeriya ta fuskar noma amma kuma akwai bukatar a kara mayar da hankali kan harkar noma.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Najeriya Sun Bayyana Ra'ayoyi Mabanbanta Kan Shirin Farfado Da Tattalin Arziki