A gurin taron, shugaba Buhari, ya yi nuni da irin muhimmanci da kuma nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun lokacin da ya karbi ragamar mulki dangane da yaki da ta’addanci da samar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma farfado da tattalin arziki.
Ana sa ran wannan sabon tsari zai taimaka wajan cika alkawarin da gwamnatin APC, ta yi na kawo cigaban kasar da farfado da tattalin arziki da kuma yaki da talauci da ya addabi ‘yan Najeriya.
Wannan sabon tsari mai manufar “Dawo da Najeriya a kan turbar ci gaba da bunkasa mai dorewa” zai kasance ginshikin kawo amfani ga kasar ta yadda ba za a koma muguwar hanyar da aka bi a bay aba, wadda ta yi sanadiyyar yanayin da kasar ke kokarin kaucewa, kamar yadda babban Malamin hulda da jama’a a fadar gwamnati, Malam Garba Shehu, ya bayyana a hirarsu wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka, Umar Faruk Musa.
Domin karin bayani saurari rahoton Umar Faruk Musa.
Facebook Forum