'Yan Najeriya Na Bayyana Ra'ayoyi Mabanbanta Kan Mulkin Buhari

Shugaba Buhari (Facebook/Femi Adesina)

Shugaba Buhari (Facebook/Femi Adesina)

Masu ruwa da tsaki da wasu ‘yan Najeriya a kusan kowane bangare na bayyana mabambantan ra’ayoyi kan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, a yayin da a ke kimanin mako biyu shugaban ya yi ban kwana da fadar gwamnatin kasar.

Ra’yoyin sun shafi cika alkawura ne ko akasin haka na mulkin Buhari a tsawon shekaru 8 da ya yi kan karagar mulki.

Kama daga alkawarin samar da tsaro da samar da aiyuka ga matasa ko farfado da tattalin arziki zuwa yaki da cin hanci da rashawa, na daga abubuwan da mutane ke cewa shugaba Buhari ya tabuka ko sam bai tabuka ba.

Musa Sarkin Adar, wanda shahararren dan Majalisar Wakilai ne kuma mai marawa shugaba Buhari baya, ya ce in a ka duba tsantsar gaskiya an samu akasi da ya hana nasarar shugaba Buhari.

Shi kuma dan kasuwa Jauro Hammadu Saleh, cewa yayi ya na takaicin yadda ya sa rai shugaban zai bunakasa tattalin arziki, amma karshe bashi ke neman durkusar da kasar.

Dan canjin kudi a Abuja, Umar Garkuwa, na da wani ra’ayin na daban da ke cewa duk barnar da a ke zargin an tabka, shugaba Buhari ya na sane kuma ya na daukar matakai iya iyawar sa don daidaita lamura.

Tun hawan sa karagar mulki, shugaba Buhari wanda ke tinkaho da goyon bayan talakawa kuma har ma talakawa suka tara gudunmawa don daukar nauyin kamfen, ya yi alwashin ba zai ci amana ba.

Shin shugaba Buhari ya ci amana ko bai ci amana ba? wa’adin mulkin sa ya zo karshe kuma tarihi za a jira a ga irin adalcin da zai yi ma sa.

Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Yan Najeriya Sun Bayyana Mabanbantan Ra’ayoyi Kan Mulkin Buhari - 2'38"