Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari, Tinubu Da Wasu Manyan Najeriya Sun Yabawa Hilda Baci Kan Kafa Tarihin Gasar Dafa Abinci tsawon Sa'o'i Ba Tare Da Tsayawa Ba


Hilda Baci
Hilda Baci

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, “Shugaba Buhari ya yaba wa matashiyar kuma kwararriya a fannin dafa abinci bisa yadda ta nuna hazaka da sha’awarta na sana’a da yin tasiri ga tattalin arziki tare da horar da wasu kan harkokin kasuwanci.

Wannan nasarar dai ta samu saƙon taya murna daga sauran manyan mutane na ƙasar.

"Ina taya Hilda Effiong Bassey murnar samun wannan gagarumar nasara. Hakika babbar manuniya ce ta 'yan Najeriya za su iya, tare kuma da bayyanar da kwarewa. Muna matukar alfahari da ita,” in ji z ababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, duk sun aika sakwannin yabawa ga matashiyar.

Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/PDP)
Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/PDP)

Mai dafa abincin 'yar shekaru 27, ta karya tarihin Lata Tandon, wata ‘yar kasar Indiya wacce ta kafa tarihin tsawon lokacin dafa abinci a duniya na Guinness da tsawon sa'o'i 87 da mintuna 45 ba tare da tsayawa ba a shekarar 2019, inda ta zama sabuwar mai rike da tarihin na "Guinness World Record".

To sai dai duk da nasarar da ta samu, har yanzu kungiyar Guinness World Records ba ta tabbatar da nasarar Hilda Baci a hukumance ba.

Wannan yanati ya jefa 'yan Najeriya da dama a halin rudani da fargaba kan dalilin da ya sa har yanzu Kungiyar Guinness ba ta amince da wannan nasarar ba.

Da yake mayar da martani a shafin Twitter, kungiyar Guinness World Records ta ce suna sane da yunkurin na ban mamaki kuma za su fara binciken dukan shaidu kafin su tabbatar da hakan a hukumance.

XS
SM
MD
LG