A cewar shugaba Muhammadu Buhari nan take dokar za ta soma aiki, ana kuma sa ran za ta taimaka wajen inganta hanyoyin takaita yaduwar annobar COVID-19 da kuma tabbatar da lafiyar 'yan Najeriya musamman a wannan lokaci da ake samun karuwar adadin masu kamuwa da cutar.
Masu ruwa da tsaki da kuma masana a fannin kiwon lafiya sun yaba da matakin. Dr. Nasiru Sani Gwarzo, daya daga cikin shugabannin kwamitin ko-ta-kwana da ke yaki da cutar COVID-19 a jihar Kano, ya ce dokar za ta tabbatar cewa duk wanda ya ke da niyyar kare kansa to zai yi amfani da wannan dama ya kare kansa, wanda kuma ya bijire za a iya amfani da wannan dama a tursasa masa har sai ya bi dokar da ta dace.
Ya ci gaba da cewa, shi ya sa ma'aikatan kiwon lafiya idan aka kafa doka suke fassara ta don ilimantar da al'umma da basu hujja da kuma zaburar da su domin su kare kansu su kare sauran jama'a.
Shi ma Dr. Muktar Aliyu ya ce kwarai da gaske wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka zai yi taimako sosai wajen rage yaduwar wannan cuta ta coronavirus saboda yin amfani da takunkumin da kuma bada tazara na cikin hanyoyin da aka gano a kimiyyance na dakile yaduwar wannan cuta.
Daga cikin sharuddan dokar, sashe na 5 ya nuna duk wanda ya saba ta za a ci shi tara ko ya fuskanci hunkucin zama gidan kaso tsawon wata shida ko duka biyu.
Khadija Abubakar 'yar Najeriya ce, ta ce ba ta tunanin rashin sanya takunkumin ya isa ya kai a ce za a kai mutun gidan yari har wata shida, matakin ya yi tsauri. Ta kara da cewa idan aka duba za a ga cewa mutane da yawa ma in suka saka takunkumin nan basa iya numfashi sosai, kamata ya yi a dan sassauta wa mutane.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya umarci hukumomin tsaro a fadin kasar su tabbatar da kiyaye wannan doka, Inda ya gargadi cewa hukunci zai hau kan duk jami’in da ya bijirewa hakan.
Aliyu Shamaki, wani mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum a Najeriya, ya ce a lokacin da aka sanya matakan kulle a wasu garuruwa, wasu sun yi korafe-korafen cewa aljihun wasu shi ke basu damar fita su yi yawo.
Tun bayan bullar wannan cuta dai a Najeriya kawo yanzu, sama da mutane dubu dari suka harbu da ita, ta kuma yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1500 a kasar.
Saurari karin bayani cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5