'Yan Najeriya na murnar nasarar da Chidinma Adetshina ta samu a gasar sarauniyar kyau ta duniya data gudana a kasar a Asabar din data gabata. saura kiris ya rage Adetshina ta lashe kambin, inda aka ayyanata a matsayin wacce ta zo ta 2 a gasar, sai dai duk da hakan an nadata a matsayin sarauniyar kyan duniya mai wakiltar nahiyoyin Afirka da Oceania
Adetshina ta samu goyon bayan miliyoyin 'yan Najeriya bayan da takaddama a kan zamanta 'yar kasa ya tilasta mata janyewa daga gasar sarauniyar kyan duniya a Afrika ta Kudu a farkon watan Agustan da ya gabata.
Mahaifin Adetshina dan Najeriya ne sannan mahaifiyarta mutuniyar Afrika ta Kudu ce mai jibi da kasar Mozambique.
Tace ta damu da aminci da walwalar iyalanta bayan da aka rika kai mata hare-haren nuna kyamar jinsi ta kafar sadarwar intanet.
Jim kadan bayan janyewarta, masu shirya gasar sarauniyar kyan Najeriya suka gayyace ta domin ta wakilci kasar mahaifinta.
A Lahadin da ta gabata, hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna ketare (NIDCOM) ta yaba da hakurin Adetshina.
Ga matasa kamarsu Ehi Maggy nasarar Chidimma yar shekaru 23 da haihuwa wani abin farin ciki ne mai karfafa gwiwa musanman ga matasa.
Ita ma Hafsat Tijjani ta ce, akwai darasi babba da ya kamata a koya bisa salon jajircewarta.
Masu tsara gasar dai sun sha jaddada cewa matakan zabar sarauniyar suna taka tsantsan inda ake tabbatar da adalci a fayyace komai kuma a fili.
Mista Abel Alhaji, wani mai sharhi kań al’amuran yau da kullum a Jamus, ya ce akwai bukatar masu shirya gasar suka kara tsabtace harkar don shawo kan takaddamar da ke tattare da gasar.
Mata dai sama da 100 daga sassa daban-daban na duniya suka shiga gasar da ta gudana a kasar Mexico inda wakiliyar kasar Denmark ta zo ta daya wakiliyar Najeriya ta zo ta biyu sai kuma wakiliyar kasar Mexico mai masaukin baki da ta zo ta uku.
A saurari rahoton Ramatu Garba Baba:
Your browser doesn’t support HTML5