‘Yan Najeriya Na Da Rawar Da Za Su Taka A Yaki Da Matsalar Tsaro – Al Mustapha

Your browser doesn’t support HTML5

Dole Kowa Ya Sa Hannu A Lamarin Tsaro A Najeriya – Al-Mustapha

Hukumomin Najeriya dai sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan matsalar ta tsaro a sassan kasar musamman a arewa maso yammaci da gabashi. 

A yayin kaddamar da wani taron neman hanyoyin wanzar da zaman lafiya a Najeriya da kungiyar neman zaman lafiya ta kasa da kasa wato IAWPA ta yi a birnin tarayya Abuja, wasu masu fada a ji sun bayyana cewa ya kamata ne duk wani mai kishin kasa ya ba da gudunmuwa wajen samar da tsaro a Najeriya.

Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon babban jami’in tsaro ne ga marigayi shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Sani Abacha, daga shekarar 1993 zuwa 1998 kuma masanin tsaro ne da ya yi fice a aikin tattara bayanan sirri.

“Lokaci ya yi da duk wani mai kishi na Najeriya da ma Afirka da kowa ya mike da kafarsa ya rika ba da gudumawa, abubuwa ba su tafiya daidai, akwai mutane da suke kashe kudadensu akan kirkiro fitinu, kuma da alama suna samun galaba.”

A halin da Najeriya ke ciki dai, duk sassan kasar kama daga arewa, yamma, gabas da tsakiya na fama da tabarbarewár tsaro ne kuma shugabanci na gari da zai kula da duk bangarorin kasar da daidaito a rabon albarkatun kasa na daga cikin mafita da za su taimaka wajen kawo karshen matsalolin tsaro in ji John Shishi, daya daga cikin masu fafutukar neman zaman lafiya a kasar.

Wasu daga cikin mahalarta taron neman zaman lafiya a Najeriya da IAWPA ta shirya

A daidai lokacin da ake zargin cewa matasa ake amfani da su wajen aikata miyagun laifuka a Najeriya, kwamared Abubakar Mailato, da ke zaman babban jagora a kungiyar matasa masu rajin wanzar da zaman lafiya da yin sulhu a cikin a’lumma a kasar ya bayana cewa akwai a yi karatun ta nutsu.

“Lallai akwai bukatar mu gyara ainihin zamantakewarmu, mu dauki matakan ganin ‘yan siya sun daina amfani da matasa domin yin abin da ya shafi bangar siyasa, da wani al’amarin da bai kamata ba kamar ba su kwaya, mu kuma gaya wa matasan nan cewa idan ‘yan siyayan nan suka kira su don su ba su ababen maye, su gaya musu su ba su ‘ya’yansu su je da su.”

A matsayinta na uwa, sarauniya Amina Temitope Ajayi, ta ce matasan Najeriya na bukatar kulawa ta musamman tare da nuna musu kauna sakamakon yadda wasu daga cikinsu ba su tashi da sanin wadannan muhimman abubuwa ba a gidajensu, sannan ta kara da cewa idan aka samu zaman lafiya zai samar da hadin kai tsakanin ‘yan kasa.

Masana tsaro da sauran masu ruwa da tsaki dai na ci gaba da yin kira ga gwamnati da ta fitar da sabbin dabarun kawo karshen matsalolin tsaro da kuma tabbatar da damawa da duk ‘yan Najeriya da daidaito don cimma nasara a yaki da ake yi da miyagun iri da ke ta'adancin kashe-kashen al’umma ba laifin tsaye balle na zaune a kasar.

Hukumomin Najeriya dai sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan matsalar ta tsaro a sassan kasar musamman a arewa maso yammaci da gabashi.

Saurari rahoton Halima AbdurRauf daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Najeriya Na Da Rawar Da Za Su Taka A Yaki Da Matsalar Tsaro – Al Mustapha - 3'54"