'Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Kuka Kan Matsalar Karancin Man Fetur

Wani dan "black market" yana sayar da man fetur a akan titin Abuja, Najeriya

Matsalar karancin man fetur na kara ta'azzara a wasu sassan Najeriya kamar yadda rahotanni ke nunawa yayin da hukumomin kasar ke zargin dillalan man da boye shi domin cin kazamar riba.

‘Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan matsalar man fetur da ta ki ci ta ki cinyewa.

Matsalar man fetur a duk karshen shekara kan bayyana a Najeriya, inda akan zargi gidajen man da boye shi.

Rahotanni da dama sun bayyana yadda masu ababan hawa da ke amfani da man fetur, suke korafin kashe makudan kudade wajen sayen man.

“Tun karfe hudu na safe nake kan layin mai, harkar mai sai dai a hanklai.” Inji wani da ya bayyana sunansa a matsayin Shehu da ya tattauna da wakilinmu Hassan Umaru Tambuwal da ke Ibadan a jihar Oyo.

Wani batu da wasu masu sayen man suka ce yana kara ta’azzara lamarin shi ne yadda masu gidajen mai suke nuna fifiko akan wasu.

“San rai ake yi, sai a rika ba masu jarka ba a ba masu babur.” Inji wani da bayyana sunansa ba.

Kamfanin matatar man fetur ta Najeriya NNPC ya dora laifin karancin man akan Dillalan man, wadanda ta ce suna boye shi domin samun kazamar riba.

Hakan ya sa hukumomi suka rika tilasta ma wasu gidajen man suna fitar da shi suna sayarwa.

A wasu lokuta ma har akan rufe wasu gidajen man a matsayin ladabtarwa saboda sun boye man.

Saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal daga Ibadan domin jin cikakken bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Kuka Kan Matsalar Karancin Man Fetur - 2'00"