Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa wato NCC ta bayar da umarnin rufe duk wani layin waya da ba a yi wa rajista da lambar shaidar zama dan kasa ta NIN ba, ko da tsohon layin waya ne, lamarin da ya sa al’ummar kasar da ke da layukan sadarwar ci gaba da maida martini game da wa’adin makonni biyu da hukumar ta bada.
Bayan haka jama'a na ci gaba da kokawa akan naira ashirin da wasu kamfanonin sadarwar ke zabtarewa yayin duba lambar shaidar dan kasa, wato NIN.
Wani ma’aikacin daya daga cikin kamfanonin sadarwar da ke Najeriya, da ya so a sakaya sunansa, ya ba wadanda ke karkara shawarar su yi amfani da lambar Code ta *785*, sai su saka lambar su ta NIN daga nan kuma su saka #. Amma ya kara da cewa wadanda basu da lambar NIN, to dole sai sun je an yi masu.
Tuni dai wasu 'yan majalisar dokokin Najeriya suko soma kokawa akan wa’adin na makonni biyu da hukumar ta NCC ta bada.
Saurari cikakken rohoton Ibrahim Abdul'Aziz:
Your browser doesn’t support HTML5