'Yan Najeriya dake kasar Nijar suna cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da cika kwanaki dari da shugaba Buhari ya dare kan kujerar mulkin kasar da ta fi kowace kasa karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.
Sun nuna farin cikinsu da yadda fargaba da tsoro suka kama masu rashin adalci koda a fannin kasuwanci ne misali kamar sayar da man fetur a kasar.
Wani dan Najeriya dake zaune a Nijar yace ko yanzu cikin kwanaki dari sai a yiwa Allah godiya domin an samu canji. Yace an samu kama manyan 'yan Boko Haram. Tattalin arziki ya fara farfadowa. Da da wuya a samu mai gidan mai amma yace ya je kuma ya samu a kudi nera dari lita daya. Da can kuwa har dari biyu suna biya.
Barayin shanu 'yanzu ana kamasu. Wani yace an samu cigaba ainun cikin dan karamin lokaci. Yayi addu'a Allah ya taimakeshi, shi shugaba Buhari. Wani dan kasuwa mai yawan tafiya yace yanzu babu mai wulakantasu a kan hanya kamar da.
Su ma 'yan Nijar sun tofa albarkacin bakinsu akan shugabancin Buhari akan nasarorin da suke gani ya samu ciki 'yan kwanaki kalilan..
Wani dake birnin Kwanni yace a fannin tsaro da cin hanci da rashawa Najeriya ta samu canji daga barnar da gwamnatin PDP ta yi cikin shekarun da tayi tana mulki. Shugaba Buhari ya hada kawunan kasashen dake makwaftaka da kasarsa akan fannin tsaro yadda Boko Haram ba zata iya cigaba da yin barna ba.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako.
Your browser doesn’t support HTML5