A Ingila iyayen 'yan matan nan 'yan makaranta su uku da aka hakikance suna kan hanyar zuwa Syria domin shiga rundunar ISIS, suna rokonsu su yiwa Allah da Annabinsa su koma gida.
'Yan matan su duka uku wadanda kawaye ne da suke zuwa wata makaranta a gabashin Landan, sun bace ne ranar talata ba tareda barin sako gameda inda suke ba. Hukumomin Biritaniya suka ce 'yan matan sun bar Ingila cikin wani jirgin kasar Turkiyya kan hanyarsa zuwa Istanbul.
Dangin 'yan matan, Shamira Begun da Amira Abase, 'yan shekaru 15 da haifuwa da kadiza Sultana, 'yar shekaru 16 d a haifuwa, duk sun barke da kuka yayinda suke bayyana fargabarsu ahira da aka yi da su a tashar talabijin ta Ingila.
'Yansandan Turkiyya sun hada karfi da takwarorinsu na Ingila wajen neman 'yan matan. Jiya Litinin, jami'an Turkiyya sun zargi Ingila saboda bata lokaci da suka yi kamin su tuntubesu batun 'yan matan.
Mukaddashin Firayim Ministan kasar Bulent Arinc ya bayyana fatar a gano 'yan matan, amma yace idan ba ganesu ba Ingila ce zata sha zargi ba hukumokin kasar a Istanbul ba.