Yau Talata ake sa ran za'a fara wani taron koli kan hanyoyin yaki damasu mummunar hali da tsatsauran ra'ayi. Taron na kwanaki uku da jami'ai daga kasashe masu yawa zasu halarta za'a gudanar da shi ne a nan birnin Washington DC.
Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya fada jiya Litinin cewa, idan ana batun yaki "da masu tsatstsauran ra'ayi ne, gwamnati bata da cikakkiyar amsa kan wannan batu". Jami'in yayi magana ne a yayinda yake kan sabon shirin fadar shugaban Amurka ta white House na habaka sabbin matakan tunkarar irin wadannan mutane.
Jami'an Amurka suka ce burin shine karfafawa jama'a guiwa su yaki irin wannan hali. Suka ce a lokacin taron kolin, wadanda suka shirya taron zasu yi magana kan irin shirye shiryen da suke aiki anan Amurka inda a biranen Boston da Los Angeles, da kuma a yankin Minneapolis St Paul.
Ana wannan taron kolin ne bada jumawa ba, bayan munanan hare hare da aka kai a Paris kan wata mujallar barkwanci, da kuma harin da aka kai a Denmark, da kuma vidiyon da 'yan kungiyar ISIS suka nuna ranar Lahadi inda suka dastse kawunan wasu Misarawa a Libya, kiristoci 'yan darikar coptic.