'Yan Matan Amurka Za Su Barje Gumi Dana Ingila Yau

Tsohuwar 'yar wasan kasar Ingila ta ce tana da imanin cewa 'yan wasan kasar su na bukatar su kare tsakiyar filinsu, a yayin karawa da za su yi tare da kasar Amurka, masu rike da kofin mata na Duniya a wasan da za su buga na kusa da na karshe a yau Talata.

Amma tshohuwar 'yar wasan Faye White, tace zai yi kyau mai horar da 'yan wasan kwallon kafa ta mata na Ingila Phil Neville, yayi amfani da hikima wajan saka Jade Moore, mai makon Keira Walsh yayin da za su kara da Amurka, a yau Talata a gasar cin kofin mata ta duniya da ake bugawa a kasar Faransa.

Kasar Amurka da take rike da kofin ta lallasa mai masaukin baki Faransa da 2-1 a wasan daf da na kusan karshe, wanda masu hasashe suke ganin cewa idan tayi nasara a wasan yau zata iya daukan kofin.

Yanzu haka kasashe hudu ne suka rage a cikin gasar, inda kasahe uku suka fito daga nahiyar turai sai kuma kasar Amurka ita kadai tilo daga wata nahiyar.

Wasan yau tsakanin Ingila da Amurka za'a buga ne da karfe 9:00 na dare, agogon Faransa, a Najeriya kuma da karfe 8:00 na dare.

Wasan gobe Netherlands (W) VS Sweden (W) wato karfe 9:00 na dare kenen agogon Faransa, a Najeriya kuma karfe 8:00 na dare.