'Yan Majalisun Tarayyar Najeriya Na Fuskantar Fushin Matasa a Wasu Jihohin Arewa

Zanga zangar matasa a harabar Majalisun Dokokin Najeriya

Ko a cikin kwankin nan sai da wasu yan majalisar dattawa dana wakilai suka gamu da fushin matasan mazabunsu a jihohin Kebbi,Katsina da kuma Bauchi,biyo bayan sa toka-sa-katsin dake wakana a tsakanin ‘yan majalisa da kuma bangaren shugaba Buhari.

Batun tantance Ibrahim Magu da batun tantance sunayen kwamishinonin hukumar zabe INEC,dake gaban yan majalisar suka harzuka wasu matasan.

To sai dai kuma masana na ganin wannan sabon salon siyasa dake da nasaba da bakar soyayya ko bakar kiyayya,na da illa ga cigaban siyasar kasar batun da Hon.Abdullahi Prembe tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Adamawa yace lamarin na da ban tsoro.

Suma dai kungiyoyin fafutuka dana cigaba sun yi tir da Allah Wadai da wannan sabon salo.

Kungiyar nagari na kowa ta Community For Peace,Corruption –Free Society,na cikin kungiyar wanzar da zaman lafiya da kuma yaki da cin hanci da rashawa a cikin al’umma, tace tir din da akan yiwa ‘yan majalisar bai fa dace ba,kamar yadda jami’in kungiyar mai kula da shiyar Adamawa Onarebul Abdulmumini Ibrahim Song ke gargadi.

Najeriya dai kasa ce mai bin tsarin demokaradiyya,dake amfani da turaku uku,wajen tafiyar da mulkin kasar,wato bangaren yan majalisa,masu tsara dokoki, da bangaren zartaswa wato bangaren shugaban kasa kana da kuma bangaren sharia,wanda kowane bangare ke da cikakken iko.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Majalisun Tarayyar Najeriya Na Fuskantar Fushin Matasa a Wasu Jihohin Arewa - 4' 01"