‘Yan Majalisun Amurka sun bayyana mabanbantan ra’yoyin kan matakin barazanar da kasar Iran ke yi, bayan da tawagar jami’an tsaron ‘kasa ta gwamnatin shugaba Donald Trump ta gabatar da bayanan sirri ga ‘yan Majalisun Amurka baki daya jiya Talata.
“Sun bayyana mana yadda barazanar kasar Iran take da banbanci da wadda aka gani a baya.. kuma kai hari kan Amurka da abokan kawancenta na nan tafe,” a cewar sanatan jam’iyyar Republican Linsey Graham na jihar South Corolina, ya fadawa ‘yan jarida bayan wata ganawar sirri da ya yi da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da mukaddashin ma’aikatar tsaro Pat Shanahan da kuma shugaban hafsan hafsoshin dakarun kasar Janar Joseph Dunford.
“akwai alamun takala daga Iran da wadanda take ingizawa,” a cewar shugaban kwamitin harkokin waje na Majalisar Wakilai, Michael McCaul na jihar Texas, ya ci gaba a cewa “tabbas muna da damuwa a kan sojojinmu wadanda ke fuskantar barazanar Iran, da kuma yiwuwar kai musu hari musamman ma a Iraki.
Sai dai kuma ra'ayin ‘yan jam’iyyar Democrats ya banbanta kan wannan batun da kuma abinda ya sa gwamnatin Trump ta ‘kara matsa lamba kan gwamnatin Iran da masu goya mata baya a gabas ta tsakiya.