'Yan Majalisu Sun Ki Amincewa da Kudurin Tattara Bayanan Sirri

Congress Gridlock Why

Badakalar fallasa bayanan sirri hukumar tsaron Amurka da wani tsohon jami'in hukumar mai suna Edward Snowden ya yi a shekarar 2012 ta bar baya da kura.

Majalisar Dattawan Amurka ta hana wani kudurin doka da majalisar wakilan kasar ta gabatar yin tasiri, wanda zai kawo karshen tattara daukacin bayanan sirrin da hukumar Tsaron Kasar ke tatsa daga tattaunawar da mutane ke yi ta wayar talho.

‘Yan majalisu 57 ne suka ki amincewa da kudirin dokar yayin da 42 suka amince a kuri’ar da aka kada a yau Asabar.

Akalla kuri’u sittin ake bukata domin amincewa dokar, wacce kusan daukancin ‘yan majalisar wakilan kasar suka amince da ita a makon da ya gabata.

Kudirin dokar, wanda aka fi sani da USA Freedom Act da harshen Ingilishi, ya samu goyon bayan ‘yan majalisar wakilai 338 idan aka kwatanta da wakilai 88 da suka ki amincewa.