Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sake Jaddada Goyon Bayanta ga Iraqi


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Biyo bayan sake kwace Ramadi da kungiyar ISIS ta yi shugaban Amurka ya sake jaddada goyon bayan kasarsa ga Iraqi

Shugaban Amurka Barack Obama ya sake jaddada kwakkwaran goyon bayan da Amurka ke baiwa Firayim Ministan Iraki Haider al-Abadi, da kuma wani sabon farmakin da dakarun da ba soji ba ke shirin kaiwa, da nufin sake kwato birnin Ramadi da ke Iraqin daga hannun mayakan kungiyar ISIS mai da'awar kafa daular Islama.

Wannan shelar ta Shugaban na Amurka, ta zo ne a yayin wata ganawa jiya Talata da manyan masu ba da shawara kan harkar tsaro, don tattaunawa kan halin da ake ciki a Iraqi, bayan da birnin na Ramadi ya fada hannun mayakan na ISIS.

Tun da farko, mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon Kanar Steve Warren, ya ce wannan yinkuri na sake kwato hedikwatar ta lardin anbar, ya dada fuskantar kalubale sanadiyyar gudun da sojojin Iraqi su ka yi su ka bar dinbin makaman Amurka a Ramadi, yayin da su ka fuskanci farmaki daga mayakan ISIS ranar Lahadi.

Waren ya ce sojojin na Iraqi sun gudu sun bar dinbin motocin sojin Amurka, ciki har da tankokin yaki, da motocin daukar mayaka masu kariya da kuma bindigogin atilare.

Sake kwato Ramadi da kungiyar ISIS ta yi, ya janyo mummunan suka ga manufofin Shugaba Barack Obama game da rikicin na Iraqi, ciki har da hare-haren jiragen sama kawai da ake kai ma 'yan ISIS, ba tare da ko da alkawarin tura sojojin Amurka na kasa su taimaki 'yan Iraqi ba.

"Tsarin Shugaban kasar bai yi tasiri," a cewar Kakakin Majalisar Wakilan Amurka John Boehner, da ke jagorantar Majalisar Wakilan, wadda 'yan Republican ke da rinjaye ciki.

To amma Mai magana da yawun Fadar Shugaban Amurka ta White House Josh Earnest, ya zargi 'yan Majalisar Tarayyar Amurka da kin bai wa Mr. Obama wata sabuwar damar da ya nema ta matakin soji, don yakar kungiyar ta ISIS.

XS
SM
MD
LG