WASHINGTON D C —
A jiya Alhamis ne majalisar dokokin Amurka ta ki amincewa da dokar ta bacin da shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana don samun kudin da zai gina wata Katanga a kan iyakar Amurka da Mexico, yayinda ‘yan majalisar dattawa 59 suka jefa kuri’ar watsi da ita, wasu 41 kuma basu goyi baya ba. Hakan ya faru ne makonni bayan da majalisar wakilai ita ma ta dauki irin wannan matakin.
‘Yan majalisar dattawa 12 ne na jam’iyyar Republican suka hada kai da ‘yan jam’iyyar Democrat wajen yin fatali da matakin a majalisar mai rinjayen ‘yan Republican.
Wannan matakin, ya yi watsi da bukatar fadar White House tare da yin biris da barazanar da shugaba Trump ke yi ta amfani da karfin ikon sa wajen cin gashin kansa kan wannan lamari.