'Yan Majalisun Amurka Sun Amince Kan Sake Kakabawa Rasha Takunkumi

Shirin dokar ya ba 'yan majalissar tarayyar Amurka damar kin amincewa da sassauta takunkumin da za a sa akan kasashen.

‘Yan majalisar Dokokin Amurka sun cimma yarjejeniyar aika wani sabon shirin dokar da ke neman saka sabbin takunkumi akan kasashen Rasha, Iran da Koriya Ta Arewa da za su turawa shugaba Donald Trump don ya sanya hannu.

Sanata Bob Corker ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi a yammacin jiya Laraba, yana mai cewa, an cimma yarjejeniyar ne bayan tattaunawar da suka yi shugaban ‘yan majalisa masu rinjaye Kevin McCarthy.

A baya da Corker bai amince a hada da Koriya Ta Arewa wajen sanya takunkumin ba, tun farko ya so a duba wannan batun a wata dokar dabam. Amma daga baya ya bar wannan zancen ya ce ‘yan majalisar wakilai za su yi aiki don duba batun Koriya Ta Arewa.

Dokor kuma ta tanadi yadda ‘yan majalissar tarayya zasu dakile duk wani kokarin da shugaba Trump zai yi don hana sanya takunkumin.