A Syria shugaban kasar Bashar al-Assad ya sake nanata kudurinsa na maida hankali wajen kawarda barazanar 'yan ta'adda a kasarsa, shugaban wanda yayi magana jiya lahadi, yace hakan ne zai kai ga samar da maslahar da 'yan kasar suke nema ga rikicin siyasar data addabe su, fiyeda shekaru hudu da rabi yanzu.
Shugaba Assad ya bayyana haka ne lokacinda wata tawagar wakilan majalisar dokokin Rasha suka gana da shi a Damascuss. Wani dan majaisar dokokin Rasha yace Assad a shirye yake ya ya gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisa muddin shine bukatar 'yan kasar.
Ma'aiatar harkokin wajen Rasha tace sakataren harkokin wajen Amurka John kerry a tattaunawar da yayi d a takwaran aikinsa na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho sunyi magana kan "damar" kulla yarjejeniyar sulhu a Syria tareda goyon bayan hukumomin kasa da kasa, da zai kunshi hukumomin kasar da kuma 'yan hamayya wadanda suke kishin kasa.